ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CIIE: Dandalin samun wadata

by CGTN Hausa
23 minutes ago
CIIE

A ranar 5 ga watan Nuwamba aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato CIIE karo na 9. Wannan biki shi ne irinsa daya tilo da wata kasa ke yi a duniya. A ganina, CIIE ya wuce bikin baje koli. Dandali ne na samun wadata da ci gaba, da hadin gwiwa da kyautata mu’amala, ba kadai tsakanin Sin da kasashen da ke halartar bikin ba, har tsakanin su mahalarta.

Idan muka mayar da hankali kan kasashen Afrika, za mu fahimci cewa, bikin na bana ya zo a daidai lokacin da ake matukar bukatarsa. Ko me ye dalili?Idan ba a manta ba, a watan Mayun bana Sin ta kaddamar da manufar soke wa kasashen Afrika 53 da ke da huldar diplomasiyya da ita harajin fito. Hakika wannan manufa za ta taka rawa wajen bunkasa harkokin cinikayya da ma bunkasa samar da kayayyaki a kasashen Afrika.

Idan kuma aka hada wannan manufa da bikin CIIE, to za mu ga cewa, Sin ta bude kofa, ta yadda ’yan kasuwar Afrika za su kara fahimtar kasar da bukatunta da masu sayayya na kasar, tare da bayar da kafar talla kyauta ga kasashen. Babban abun sha’awa shi ne, wannan dandali bai takaita tallar ga Sinawa masu sayayya kadai ba, har ma a tsakaninsu mahalarta na kasa da kasa.

ADVERTISEMENT

Ba kasuwar kayayyaki kadai kasar Sin ta samar wa kasashen Afrika ba, ta samar da hanyar da kasashen za su kyautata tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Watau idan ’yan kasuwa suka samu damar fitar da kayayyaki, to hakan zai farfado da ayyukan masana’antu da samar da aikin yi, lamarin da zai daidaita al’amura da dama, tare da bunkasa tattalin arzikin kasashe. Kun ga ta hakan, kasashen sun samu damar samun ci gaba, bisa dogaro da albarkatu da karfinsu.

Hakika kasar Sin tana samar wa kasashen duniya dimbin damarmaki na samun ci gaba ba tare da nuna wariya ko kyashi ba. Kuma wadanda suka fi amfana da manufofinta na tallafi da gata su ne kasashen Afrika, lamarin da ya nuna karara cewa, burinta shi ne ganin ci gaban kasashe masu tasowa da tabbatar da adalci da daidaito da wadata da kwanciyar hankali masu dorewa a fadin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Iliana Iotova Murnar Zabenta A Matsayin Shugabar Kasar Bulgaria

Li Qiang Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Majalisar Gudanarwar Sin

CIIE
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

MASU ALAKA

Xi Ya Taya Iliana Iotova Murnar Zabenta A Matsayin Shugabar Kasar Bulgaria
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Iliana Iotova Murnar Zabenta A Matsayin Shugabar Kasar Bulgaria

November 9, 2026
Li Qiang Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Majalisar Gudanarwar Sin
Daga Birnin Sin

Li Qiang Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Majalisar Gudanarwar Sin

November 9, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

November 8, 2026
Next Post
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

ADC Ta Yi Hasashen Kayar Da Tinubu A 2027, Ta Zargi APC Da Kai Wa ’Yan Adawa Hari

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

ADC Ta Yi Hasashen Kayar Da Tinubu A 2027, Ta Zargi APC Da Kai Wa ’Yan Adawa Hari

November 9, 2026
CIIE: Dandalin samun wadata

CIIE: Dandalin samun wadata

November 9, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

SERAP Ta Bukaci Gwamnati Ta Yi Cikakken Bayani Kan Rabon Tallafin N50,000

November 9, 2026
Xi Ya Taya Iliana Iotova Murnar Zabenta A Matsayin Shugabar Kasar Bulgaria

Xi Ya Taya Iliana Iotova Murnar Zabenta A Matsayin Shugabar Kasar Bulgaria

November 9, 2026
Ɓarayi Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

Ɓarayi Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

November 9, 2026
Li Qiang Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Majalisar Gudanarwar Sin

Li Qiang Ya Sanya Hannu Kan Umarnin Majalisar Gudanarwar Sin

November 9, 2026
Gwamnatin Nasarawa Ta Yi Gargaɗi Kan Masu Amfani Da Siyasa Wajen Haddasa Rikici

Gwamnatin Nasarawa Ta Yi Gargaɗi Kan Masu Amfani Da Siyasa Wajen Haddasa Rikici

November 9, 2026
Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe

Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe

November 9, 2026
Yadda Masu Amfani Da Wema Bank Za Su Duba Cancantar Samun Tallafin 50,000

Yadda Masu Amfani Da Wema Bank Za Su Duba Cancantar Samun Tallafin 50,000

November 9, 2026
Ku Daina Amfani Da Kotu Wajen Hana Mu Takara A 2027 ADC Ga APC

Ku Daina Amfani Da Kotu Wajen Hana Mu Takara A 2027 ADC Ga APC

November 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.