A yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam na gwaji zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba taurarin dan adam ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar.
An harba tauraron dan Adam na gwaji na tsarin musayar bayanai (VDES), ta hanyar amfani rokar Kuaizhou-11 Y2 da misalin karfe 9 da mituna 15 na safe agogon birnin Beijing, ya kuma shiga cikin falaki kamar yadda aka tsara.
Za a yi amfani da tauraron ne, wajen gwajin sadarwa da tabbatar da muhimman fasahohin VDES da tsarin tantancewa mai sarrafa kansa (AIS).
A cewar cibiyar harba taurarin, wannan shi ne karo na 23 da aka yi amfani da rokokin Kuaizhou-11 wajen harba taurarin dan-Adam.(Ibrahim)