Jagoran rikon kwarya na tawagar Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin ta jinjina yadda kasashen dake yankin manyan tafkunan Afirka suka karfafa hadin gwiwa wajen magance kalubalen tsaro tare, da sa kaimi ga hadin gwiwa a yankin, da kuma samun ci gaba mai dorewa, da warware matsaloli ta hanyoyi mafiya dacewa da su. Wannan ya bayyana hikima da juriya da suke da su.
A yayin taron da kwamitin sulhun MDD ya shirya a fili kan halin da ake ciki a yankin manyan tafkunan Afirka, Dai Bing ya ce da a bi manufar a tsira tare a gudu tare, za a iya tinkarar barazanar tsaro yadda ya kamata.
Don haka ya dace kasashen yankin su ci gaba da bin hanyar da ta dace ta kiyaye tsaro tare, da warware sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa, da tuntubar juna kan mutunta muradu da damuwar juna.
Dai Bing ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su nuna goyon bayan matakan soja ko mataka ba iri na soja ba, don kawar da barazanar tsaro a yankin cikin gaggawa.
Bugu da kari, cin moriyar albarkatun kasa ba bisa ka’ida ba, abu ne mai muhimmanci dake illatar zaman lafiya a yankin. Don haka ya zama dole kasashen duniya su yi aiki tare, don aiwatar da matsaya daya da aka samu a yayin babban taron karawa juna sani kan yadda za a yi amfani da albarkatun kasa da aka shirya a birnin Khartoum a shekarar 2021.
Kaza lika wajibi ne a katse hanyoyin hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba da wasu kungiyoyin ta’addanci, da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai, suke amfani da su.
Sannan ya kamata abunkasa harkokin kasuwanci bisa doka, ta yadda albarkatun kasa za su zama muhimmin abu dake jawo hankulan mutane wajen saka hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. (Mai Fassarawa: Safiyah Ma)