A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama.
An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar da rahotanni da dama a baya-bayan nan, inda ta bayyana cewa, ayyukan hakar ma’adinai, da gandun dazuzzuka da kamun kifi da kasar Sin ke yi a yammacin Afirka, sun haifar da mummunar illa ga muhallin halittu, tare da yin kira ga yankin yammacin Afirka da ya ba da hadin kai wajen karfafa sa ido kan lamarin.
A yayin da yake mayar da martani, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin na gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka bisa ka’idojin gaskiya, da zuciya daya da kyakkyawar manufa, da kuma kyakkyawan ra’ayi na adalci da cin moriya, don ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka da samun habaka mai dorewa, wanda gwamnatoci da jama’ar Afirka suka yi maraba da su.
Ya kara da cewa, babban abin da Afirka ke sha’awa na yin hadin gwiwa da kasar Sin shi ne bayar da misali ta fuskar samun moriyar juna da samun nasara ga bangarorin biyu. A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana bukatar kamfanonin kasar Sin da ofisoshin kasuwanci na ketare da su mutunta dokokin da suka dace da hakan. Har ila yau, za ta ci gaba da jagorantar masana’antu don aiwatar da manufar bunkasa muhalli, da shigar da kiyaye muhalli a cikin dukkan matakan tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














