A yau Lahadi, kasar Sin ta gabatar da jerin matakan kara kyautata manufar mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido domin biyan bukatunsu da inganta sayayya a cikin gida.
Wata sanarwa da ma’aikatar kula da cinikayya da wasu sassan gwamnati 5 na kasar Sin suka fitar, ta bayyana rage mafi karancin adadin kudin sayayya dake bukatar mayar da kudin haraji ga matafiya, lamarin da zai ba baki matafiya damar neman a mayar musu da akalla kudin Sin RMB yuan 200, kimanin dalar Amurka 27.75 a kanti guda a kuma rana guda, idan suka cika sharudan da aka gindaya.
- Karon Farko Sin Ta Fi Samar Da Wutar Lantarki Ta Aiki Da Makamashin Nukiliya A Duniya
- Kungiya Ta Bai Wa Marayu Tallafin Atamfofi Da Shaddodi A Yobe
Yayin da ake tabbatar da magance duk wata barazana, za a iya mayar da kudi ta hanyoyi daban daban ciki har da na wayar salula da katin banki da kuma tsabar kudi, domin samar da hanyoyi masu dacewa na biyan kudi ga baki matafiya. Iyakacin abun da za a iya mayarwa a tsabar kudin shi ne yuan 20,000.
Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki.
Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp