Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis.
Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, kakaba karin haraji da Amurka ta yi ita kadai, ta yi matukar saba wa ka’idojin kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO, wanda ke nuni baro-baro a fili da ra’ayi na kashin kai da gicciye kariyar ciniki.
Don haka, a cewar jami’ar ma’aikatar, yunkurin na Amurka ya yi matukar kawo cikas ga tsarin gudanar da ciniki a tsakanin bangarori daban-daban, da yin kafar ungulu ga harkokin masana’antu da tsare-tsaren samar da kayayyaki a duniya, da kuma ta’azzara rikicin ciniki a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp