Ma’aikatar kula da harkokin al’umma ta kasar Sin ta lashi takobin karfafa hidimomin kula da tsoffi a kasar, domin al’ummar kasar da suka manyanta.
Ministan ma’aikatar Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya Litinin cewa, ma’aikatar ta kafa wani tsari mai matakai 3 na bayar da hidimomin kula da tsoffi da zai hada gundumomi da garuruwa da kauyuka.
- Zargin Ta’addanci A Zamfara: Matawalle Ya Ƙalubalanci Gwamna Dauda Su Yi Rantsuwa Da Alƙur’ani
- Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya
A cewar Lu Zhiyuan, domin amfana da tsarin samar da hidimomin, za a karfafa tare da kyautata cibiyoyin kula da tsoffi dake unguwanni. Ya ce wadannan cibiyoyin za su samar da taimakon abinci da na kiwon lafiya da na bukatun gaggawa a matsayin wani bangare na kula da tsoffi a gidajensu, wanda zai karfafa tubalin wannan bangare.
Har ila yau, domin karfafa bangaren kula da tsoffin, ministan ya ce za a yi kokarin tallafawa tare da samar da kwararru da kayayyakin kula da tsoffi da fadada amfana da hidimomin da kuma kara raya tattalin arzkin bangaren hidimtawa tsoffi. (Fa’iza Mustapha)