Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, bayan shugaban kasar Amurka ya yi barazanar kakaba karin harajin kaso 50 kan kayayyakin kasar Sin.
Yayin taron manema labarai na yau Talata, kakakin ma’aikatar Lin Jian, ya ce, idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya da na haraji, to Sin ba za ta saurara ma ta ba.
- Sojoji 2 Da ’Yan Ta’adda Da Dama Sun Rasu A Wani Gumurzu A Borno
- Gwamnan Kano Ya Sadaukar Da Lambar Yabonsa Ga ‘Ya’yan Marasa Ƙarfi A Nijeriya
A cewar Lin Jian, yadda Amurka take ta kakaba haraji kan kasashe ba tare da bambance su ba, ya yi matukar take ‘yanci da muradun kasashen da ma ka’idojin cinikayya na hukumar kula da cinikayya ta duniya da tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa bisa doka, da kuma yin mummunan tasiri kan tsarin tattalin arzikin duniya.
Ya kara da cewa, wannan ra’ayi ne na yin gaban kai wajen daukar mataki ba tare da la’akari da sauran bangarori ba, haka kuma kariyar cinikayya ne da cin zali a bangaren tattalin arziki, wanda kasa da kasa suka yi tir da shi.
Game da ko Sin da Amurka sun tattauna ko sun tuntubi juna game da batun, Lin Jian ya ce, idan da gaske Amurka na son tattaunawa, ya kamata ta nuna girmamawa da adalci da kuma saka alheri da alheri. (Fa’iza Msutapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp