Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sha nanata cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya dogara a kan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen ketare fiye da kima, kuma Amurka na neman yin ciniki bisa adalci da daidaito. Sai dai kuma, da yake mayar da martani a yau Litinin 10 ga watan Maris, yayin wani taron manema labaru na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta yi nuni da cewa, maganar da ake yi a kullum kan “rasa madafa” da neman cikakken daidaiton cinikayya ta saba wa ilimin tattalin arziki na asali, da yin watsi da hukunci da muradun kamfanoni da masu sayayya na Amurka.
Mao Ning ta ce, halin da ake ciki na cinikayya a tsakanin Amurka da kasar Sin yanzu haka ya samo asali ne sakamakon rawar da kasuwanni ke takawa, kuma abubuwa da dama sun shafi tsarin tattalin arzikin kasashen biyu,da manufofin ciniki da kuma matsayin dalar Amurka.
Ta kara da cewa, kasar Sin ba ta taba neman cin bulus da gangan ba. Hasali ma, Amurka ce ta fi tsintar dami a kala daga cinikayyarta da Sin. Mao Ning ta jaddada cewa, ba a sauya wa tuwo suna, domin ko ta yaya Amurka ta sauya akalar abin, ba za ta iya boye yunkurinta na siyasantarwa da mayar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a matsayin makamin dakilewa da neman murkushe kasar Sin ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp