Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya musanta zargin da wakilin Amurka ya yi, yayin wani taro na kwamitin sulhun MDD game da sauyin yanayi da tsaro.
A taron na jiya, wakilin Amurka ya yi magana sau biyu, inda ya zargi kasar Sin da fitar da tarin hayakin carbon, yana zargin cewa kasar ta Sin “ta samu fa’idodin tattalin arziki ta hanyoyin da ba su dace ba, kuma tana gurbata muhalli”, yayin da a daya hannun ya yabi manufofin muhalli na Amurka, yana mai cewa sun yi nasara kuma su ne “abun koyi” ga sauran kasashe.
Game da hakan, Geng Shuang ya mayar da martani sau biyu, inda ya musanta zargin da wakilin na Amurka ya yi. Ya nuna cewa, kasar Sin ita ce kasar da aka amince da ita a duniya a matsayin mafi kwarin gwiwa, mafi karfi, kuma mafi tasiri wajen cika alkawuran rage fitar da hayakin carbon. Ya kuma kara da cewa, idan aka dubi Amurka, za a ga yadda ta zamo kan gaba wajen fitar da mafi yawan iska mai dumama yanayi a tarihi.
Bugu da kari, Amurka ta bayyana a fili cewa batun sauyin yanayi shi ne mafi girman yaudara da aka yi a tarihin dan Adam, kuma ta fice daga “Yarjejeniyar Paris” sau biyu, wanda hakan ya yi mummunar illa ga kokarin al’ummun duniya na kyautata yanayin duniya, kana ta zama babban cikas ga hadin gwiwar duniya a fannin magance sauyin yanayi.
Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, a kan batun magance sauyin yanayi, abun da al’ummar duniya ke bukata shi ne dunkulewa da hadin gwiwa, ba zargi da dora laifi kan wasu ba. (Amina Xu)














