A yau Litinin, kasar Sin ta sake jaddada kin amincewarta da matakan da suka saba wa doka da kuma tauye hakki da muradun wasu kasashe ta hanyar nuna dabi’un tilastawa da babakere ko kuma cin zarafi a fannin tattalin arziki.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Guo Jiakun ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa wata tambayar da manema labarai suka yi dangane da shirin da kamfanin CK Hutchison Holdings Limited ke yi na sayar da wasu kadarorinsa na tashar jiragen ruwa ga rukunin kamfanonin BlackRock.
- Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
- Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
A yayin taron manema labarun wanda aka saba yi a-kai-a-kai, Guo ya ce, “Mun lura da rahotannin da suke magana a kan hakan”, inda ya kara da cewa, “Hukumar kula da kasuwanni ta gwamnatin kasa tana sane da yarjejeniyar kuma za ta gudanar da nazari bisa doka don tabbatar da adalci ta fuskar gasar kasuwanci da kare muradun jama’a.”
Guo ya jaddada cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana adawa da yadda ake amfani da tursasawa da cin zarafi wajen keta hakki da danne muradun wasu kasashe a fannin tattalin arziki.
Yayin da yake mayar da jawabi kan samun nasarar halartar shugabannin ’yan kasuwa na kasashen waje a taron da kasar Sin ta karbi bakunci, ciki har da dandalin raya kasa na kasar Sin, da dandalin Boao na Asiya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin na ci gaba da kokarin zurfafa gyare-gyare da kuma kara bude kofa ga kasashen waje a mataki na kololo.
Ya ce, bisa tagomashin katafariyar kasuwarta, da kyawawan manufofin da ake tsammani, da ingantaccen yanayin kasuwanci, Sin na ci gaba da zama kasa mai albarka ga kamfanonin kasa da kasa su zo su zuba jari domin samun bunkasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp