Kamfanonin aikewa da sakonni na kasar Sin sun samu aikin mika kunshin sakonni mafi girma da suka kai adadin miliyan 701 a ranar Litinin, ranar da aka fi cin kasuwar bikin sayayya mai lakabin “Double 11”, kamar yadda bayanai daga ofishin gwamnati mai kula da harkokin aikewa da sakonni suka nuna a jiya Talata.
Adadin ya karu da ninki 1.51 a kan yadda aka saba gani a cinikin yau da kullum, kana ya karu da kashi 9.7 cikin dari a kason da ake samu na shekara.
- Wakilin Sin Ya Bukaci Isra’ila Da Ta Dakatar Da Amfani Da Agajin Jin Kai A Gaza A Matsayin Hanyar Cimma Bukatar Kashin Kai
- Babban Jami’in Sin Ya Halarci Taron Kolin Shugabannin Kasa Da Kasa Kan Daukar Matakan Daidaita Sauyin Yanayi
Hada-hadar kasuwancin masu kai sako ta samu koma-baya saboda yadda kwastamomi ke ci gaba da nuna muradin sayayya ta shafin intanet. Sai dai kuma, a daya bangaren, hakan ya karfafa samun ci gaban bukatun da ake da su na cikin gida da kara kuzarin murmurewar tattalin arzikin kasa.
Wanda aka fara gabatarwa a shekarar 2009, bikin sayayya na “Double 11” na ci gaba da kyautata harkokin kashe kudi a daya daga cikin manyan kasuwannin da masu bukatu ke sayayya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)