Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba.
Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar.
Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin moriyar tsoffi ga iyalai miliyan 2.24 dake da tsoffin da suke fuskantar matsaloli.
Ya kara da cewa, kasar Sin ta kuma samar da tsare-tsaren hidimomin kula da tsoffi guda 500 a cikin unguwanni da wasu unguwanni masu dacewa da zaman tsoffi guda 2,990 da kuma dakunan cin abinci 86,000 ga tsoffin. (Fa’iza Mustapha)














