Kasar Sin ta shirya gudanar da aikin tattaro samfura daga duniyar Mars tare da dawowa duniyar dan adam a shekarar 2031, inda babban burinta na kimiyya ya kasance binciken alamomin rayuwa a duniyar ta Mars.
Dakin gwaji da bincike mai zurfi kan sararin samaniya na kasar Sin ne ya bayyana hakan, inda ya ce kasar na shirin gudanar da aikin binciken duniyar Mars mai suna Tianwen-3, ta hanyar harba kumbuna biyu a shekarar 2028. Cikin aikin da za a gudanar a lokaci guda, kumbunan za su sauka, su tattaro samfura tare da kawo su duniyar dan adam, inda wajen saukar zai kasance inda za su tattaro samfuran.
Kumbunan Tianwen-3 za su dauki wasu kayayyakin aiki da aka samar ta hanyar hadin gwiwar kasa da kasa, kana kasar Sin za ta hada hannu da masana kimiyya daga fadin duniya wajen gudanar da bincike kan samfura da bayanan da aka samo daga duniyar ta Mars. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)