Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya soki Japan game da yunkurin yin rufa-rufa da rashin daukar kalamai na takala da firaministar kasar Sanae Takaichi ta furta game da yankin Taiwan na Sin da muhimmanci, yana mai kiran hakan a matsayin yaudarar kai da ba za a amince da shi ba.
Guo Jiakun ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Alhamis cewa, ikirarin da firaminista Takaichi ta yi cewa za ta kauracewa yin tsokaci kan wasu batutuwa a nan gaba, ba daya yake da janye kalamai marasa dacewa da ta furta ba.
Guo Jiakun ya bayyana hakan da rashin wayo, inda ya ce Sin ba za ta taba amincewa da shi ba.
Har ila yau a yau Alhamis, ma’aikatar tsaron kasar Sin ta gargadi Japan cewa idan ta kuskura ta wuce gona da iri ta sanya kanta cikin matsala, to za ta dandana kudarta.
Kakakin ma’aikatar, Jiang Bin, ya ce batun Taiwan batu ne na cikin gidan kasar, kuma yadda za a warware shi ba shi da alaka da Japan.
Jiang Bin ya bayyana haka ne a martaninsa game da shirin Japan na girke makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a tsibirin Yonaguni, mai tazarar kilomita 110 daga gabashin yankin Taiwan. (FMM)














