Hukumomin kasar Sin, sun ware yuan miliyan 270, kwatankwacin dala miliyan 38.07 daga babban asusun tallafin rage radadin ibtila’i, domin tallafawa ayyukan ceto da na agaji a yankunan da ambaliya da guguwa suka aukuwa.
Ma’aikatar kula da harkokin kudi da ta kula da agajin gaggawa ne suka ware kudin.
An kuma raba kudin ga lardunan Hainan da Guangdong da Yunnan tare da jihar Guangxi, yayin da guguwar Yagi, irinta ta 11 a bana, ta haifar da mamakon ruwan sama da ambaliya a wadannan yankuna.
Za a yi amfani da kudin ne wajen gudanar da ayyukan ceto da agaji, inda za a mayar da hankali kan bincike da ceto da sake tsugunar da wadanda lamarin ya shafa da gano sauran barnar da ibtila’i ka iya haifarwa da gyara gidajen da suka lalace da sauransu. (Fa’iza Mustapha)