A ranar 9 ga watan Agusta ne kasar Sin ta daukaka kara kan matakan wucin gadi da Tarayyar Turai EU ta dauka kan motocin lantarki na kasar Sin, zuwa tsarin warware takaddama na kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, domin kare hakkin ci gaban masana’antar kera motocin lantarki da kuma hadin gwiwar raya kasa da kasa ba tare da gurbata muhalli ba.
Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ne ya bayyana hakan a yau Jumma’a, inda ya ce, hukuncin farko na EU dangane da batun wai gwamnatin Sin ta samar da rangwame kan motocin lantarki na kasar, ba shi da tushe na gaskiya da doka, kuma ya sabawa ka’idojin WTO da kuma cutar da yanayin hadin gwiwar duniya baki daya kan sauyin yanayi. Kasar Sin ta bukaci EU da ta gaggauta gyara kurakuranta, tare da kiyaye hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da EU, da kuma kwanciyar hankalin tsarin kera da kuma samar da motocin lantarki. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp