Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
Rahotanni daga kungiyar sa kaimi ga cinikayya ta kasar Sin, za a gudanar da taron koli na shugabannin harkokin masana’antu,...
Rahotanni daga kungiyar sa kaimi ga cinikayya ta kasar Sin, za a gudanar da taron koli na shugabannin harkokin masana’antu,...
Gwamnatin Amurka ta miƙa wasu sabbin kayan aikin soji ga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, domin ƙarfafa ƙarfin ƙasar wajen...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, wanda a cikinsa ya bukaci a kara azamar dakile...
A yau Laraba 9 ga watan Satumba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ko kadan kasar Sin ba ta taba...
Albarkacin ranar malaman makaranta ta kasar Sin wadda ake bikinta a duk ranar 10 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin...
Ana wa matasa kirari daban-daban a cikin al’umma, tun daga lokacin yarinta da ake ce musu “yara manyan gobe” har...
An bude bikin cinikayyar hidimomi ta kasar Sin ko CIFTIS a yau Laraba a birnin Beijing.Bikin zai ci gaba da...
A yau 9 ga watan Satumba, an gudanar da aikin koyarwa na "Ajin tashar sararin samaniya na Hong Kong da Macau" a...
Jami'an gwamnati, da masana, da wakilan 'yan kasuwa da 'yan jarida sama da 300 daga kasashe 33 ne suka taru jiya Talata a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, domin tattaunawa kan kwarewar shugabanci a fannonin tsaro, da ci gaba, da kuma kyautata zamantakewar al'umma. Wannan taro, wanda aka yi wa lakabi da "Taron Abota da Musaya na Xinjiang tare da Manyan Baki na Duniya," ya kuma tattaro wakilai daga Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) da Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO) wuri guda. An gudanar da taron ne karkashin taken "Kwarewar Xinjiang Wajen Iya Shugabanci da Muhimmancinta a Matakin Duniya." Babban sakataren kungiyar SCO, Nurlan Yermekbayev, ya ce a yayin da ya ziyarci Xinjiang a lokuta da dama, ya ganewa idonsa irin manyan sauye-sauyen da aka samu a yankin. Yermekbayev ya ce, hadin gwiwa tsakanin tsaro da tattalin arziki yana karfafa juna, da taimakawa wajen samar da yanayin dorewar musaya a tsakanin kasa da kasa da kuma hadin gwiwa a cikin gida. Ya kuma yi kira da a kara shimfida ayyuka masu alfanu wadanda za su iya samar da cin moriyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.