Babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin dake Geneva Mr. Chen Xu a jiya Alhamis ya yi kira ga hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kara mai da hankali kan batun zuba ruwan dagwalon nukiliyar Japan a cikin teku, kana ya bukaci kasar Japan da ta gaggauta dakatar da zubar da ruwan dagwalon a cikin teku.
Chen Xu, shugaban tawagar kasar Sin dake MDD a birnin Geneva, ya bayyana a yayin wata tattaunawa da wakilin MDD kan batun hakkin dan Adam da tsaftar ruwan sha da tsaftar muhalli cewa, idan da gaske ne ruwan dagwalon nukiliya na Fukushima ba ta da hadari, Japan ba za ta zubar da ita a cikin teku ba — kuma tabbas bai kamata ta zubar da ruwan a cikin teku ba.
Chen ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Japan da son ranta da karfin tsiya ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya ta Fukushima cikin teku, wanda hakan ya yi matukar tauye hakkin kiwon lafiya, da ci gaba da muhallin jama’a a kasashen dake gabar tekun Pasifik da ma duniya baki daya. (Yahaya Yaya)