Da karfe 3 da mintuna 8 na sanyin safiyar yau Talata 26 ga watan Agusta ne kasar Sin ta yi nasarar harba rukunin taurarin dan adam 10, ta amfani da rokar dakon kaya samfurin CZ-8A, daga cibiyar harba kumbuna ta lardin Hainan.
Taurarin da aka harba sun yi nasarar shiga falakinsu kamar yadda aka tsara, wanda hakan ya tabbatar da cikakkiyar nasarar aikin. (Amina Xu)