Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce bai dace ba, kuma bai kamata a nemi kasar Sin ta shiga tattaunawar kwance damarar makaman nukiliya tare da Amurka da Rasha ba.
Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai na yau Laraba, lokacin da yake mayar da martani game da rahotannin dake cewa, a baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa da Rasha suna tattauna batun rage makamansu na nukiliya, kuma yana fatan kasar Sin ma za ta shiga tattaunawar.
A cewar Guo Jiakun, ko kadan, karfin nukliyar Sin bai kama kafar na Amurka ba. Kuma manufarsu kan nukiliya da ma yanayinsu na tsaro ta fuskar yanki da barazanar da za su iya fuskanta, sun sha bamban da juna.
Da yake bayyana Sin a matsayin mai bin manufar kaucewa fara amfani da makaman nukiliya da yadda manufarta ta nukiliyar ke mayar da hankali kan kare kai, kakakin ya ce kasar Sin za ta ci gaba da tabbatar da karfinta na nukiliya ya tsaya a matsakaicin mataki da ake bukata na tsaron kasa, kuma ba za ta taba shiga takarar makamai da wata kasa ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp