Kudin shigar da aka samu a kasar Sin daga fim din Cartoon mai suna “Zootopia 2” da aka fara gabatarwa a duk fadin duniya tun daga ranar 26 ga Nuwamba, ya wuce kudin Sin yuan biliyan 2, wanda ya karya bajimtar fina-finai na Cartoon da aka shigo da su kasar Sin, adadin kuma ya fi na kasuwar arewacin Amurka yawa, inda kasar Sin ta zama babbar mashigar kudi a duniya dalilin wannan fim.
Kafin a nuna fim din, kamfanin da ya gabatar da shi ya yi hadin gwiwa da kamfanin gabatar da fina-finai na Shanghai don nuna gajeren fim na gabatarwa, wanda ya samu karbuwa matuka a shafukan sada zumunta ta yanar gizo, kuma ya samar da ingantaccen talla, da nuna amincewar duniya ga masana’antar fim ta Sin.
Girman kasuwar fina-finai na Sin mai bude kofa dake cike da kuzari, ta zama dandali mai albarka na hadin gwiwar fina-finai a duniya, tana samar da haske da inuwa ga cudanyar mabambantan al’adu da lalubo hanyoyin hadin gwiwar mabambantan al’adu. (Amina Xu)














