Kasar Sin ta gabatar da kundin ayyukan gwamnati da za a fi ba su fifiko a shekarar 2025 a ranar Lahadin nan, inda ta bayyana muhimman fannonin zurfafa gyare-gyare a yankunan karkara, da daukar kwararan matakai na inganta raya yankunan karkarar.
Wanda ya kasance a matsayin sanarwar farko ta manufofin gwamnati da mahukuntan tsakiya na kasar Sin suke fitarwa a kowace shekara, kundin ana daukarsa a matsayin manunin muhimman manufofin da gwamnati za ta fi bai wa fifiko.
- Amurka Ta Zama Jagorar Bata Ka’idoji Da Dokar Duniya Bisa Amfani Da Makamin Harajin Kwastam
- Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
Kundin ya yi kira da a kara matsa kaimi a kan ayyukan da suka shafi noma, da yankunan karkara da kuma manoma a shekarar 2025, da nufin ci gaba da raya yankunan karkara tare da kara karfafa tushen noma a kasar.
Kundin ya kuma bayyana cewa, idan aka yi garambawul tare da bude kofa, da kuma amfani da sabbin fasahohin kimiyya da fasaha a matsayin ginshikai, tabbas kasar za ta ci gaba da kiyaye samun wadatar hatsi tare da tabbatar da cewa, ba za a samu wani babban koma baya ko mayar da hannun agogo baya wajen yaki da talauci ba.
Kazalika, kundin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta yi iya kokarinta wajen inganta aikin gona, da karfafa yankunan karkara, da kara samar da kudin shiga ga manoma, ta yadda za ta aza harsashi mai kwari na bunkasa zamanintarwa irin na kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)