Rahotannin da aka ruwaito sun bayyana cewa, sakatariyar baitulmalin Amurka, Janet Yellen ta bayyana cewa, matakan da kasar Sin ke dauka na kandagarkin annobar COVID-19, na haifar da illa ga makomar tattalin arzikin duniya.
Game da irin wannan furuci nata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kalamai ne maras tushe balle makama.
Zhao ya ce, tun barkewar annobar ya zuwa yanzu, kasar Sin tana daukar matakan da suka dace don tinkarar annobar, a yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasar, a wani kokari na bayar da muhimmiyar gudummawa ga tabbatar da samar da isassun kayayyaki da habaka tattalin arzikin duk duniya.
A shekara ta 2021, jimillar kudin shige da ficen kayayyakin kasar Sin sun zarce dala tiriliyan 6, adadin ya kai matsayin koli a tarihi. Kana, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, yawan hajojin da aka yi shige da ficen su a kasar Sin, ya karu da kaso 9.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Ke nan, kasar Sin tana ci gaba da samarwa duk duniya hajojin ta masu inganci da rahusa.
Zhao ya kuma bukaci jami’an gwamnatin Amurka, da su dakatar da yin irin wannan furuci maras tushe, har da wadanda suke shafawa kasar Sin bakin fenti. Maimakon haka, ya dace su kara aikata abubuwan alheri, domin karfafa hadin-gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar COVID-19, da samar da ci gaba ga duk duniya baki daya. (Murtala Zhang)