Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce, yunkurin Amurka na takaita karfin TikTok na sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasa da kasa da haifar da tsaiko ga tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, lamarin da kuma zai yi illa ga ita kanta Amurkar.
Wang Wenbin ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Laraba, bayan an nemi jin ta-bakinsa kan kuri’ar yuwuwar dakatar da TikTok da ‘yan majalisar dokokin Amurka za su kada. A cewarsa, a baya-bayan nan, Amurka ta nace kan kokarinta na danne TikTok, duk da cewa ba ta taba samun wata hujja dake tabbatar da TikTok din na barazana ga tsaron kasar ba.
Ya kara da cewa, irin wannan cin zali, wanda ke hana takara mai adalci, na haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci na kamfanoni, da sanyaya gwiwar masu zuba jari na kasa da kasa da kuma haifar da tsaiko ga tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya. (Fa’iza Mustapha)