Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta amsa tambayar da aka yi mata, game da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a yau Litinin 20 ga wata, inda ta ce, Sin za ta kara maida hankali kan samar da ci gaba mai inganci, tare da fadada bude kofa ga kasashen ketare, da kiyaye murmurewar tattalin arziki, ta yadda za ta kara haifar da abubuwan mamaki ga tattalin arzikin duniya.
Rahotannin sun ruwaito cewa, babban masanin tattalin arziki na asusun bada lamuni na duniya wato IMF, Pierre-Olivier Gourinchas, ya ce kasar Sin ta sanar da samun karuwar tattalin arziki na kaso 5 bisa dari a shekarar 2024, wanda ya zarce hasashen da IMF ya yi, kana abu ne mai ban mamaki. Kaza lika, IMF ya kyautata hasashensa kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar nan ta 2025, da 2026 mai zuwa. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp