Hukumar Kwastam ta kasar Sin ta sanar a yau Jumma’a cewa za ta dage dakatarwar da ta yi kan shigo da waken soya daga kamfanoni uku na Amurka, ciki har da CHS Inc., wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga Nuwamba.
A cewar wata sanarwa daga Babbar Hukumar Kwastam ta kasar (GAC), an yanke shawarar dawo da cancantar wadannan kamfanonin ne bisa kimanta irin matakan gyara da bangaren Amurka ya dauka da kuma la’akari da dokoki da ka’idojin kasar Sin da suka dace da hakan, da kuma sharuddan tabbatar da ingancin lafiyar hatsi da tsirrai na duniya.
A wata sanarwa har ila yau, hukumar GAC ta ce kasar Sin za ta kuma ci gaba da shigo da yankakkun itatuwan konawa masu kauri daga Amurka a ranar 10 ga Nuwamba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














