Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar za ta kara inganta kula da duk wani abu mai nasaba da sarrafawa ko samarwa a bangaren ma’adanan kasa masu matukar muhimmanci, don hana fitarwa ba bisa ka’ida ba, da kuma kiyaye tsaron kasa.
Mai magana da yawun ma’aikatar wanda ya bayyana haka a yau Laraba, ya ce, karfafa yadda ake kula da fitar da albarkatun ma’adanai masu muhimmanci zuwa ketare yana da muhimmanci ga tsaron kasa da muradun ci gaba.
- Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
- JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025
A ranar Litinin da ta gabata ne, wani taron kasa da aka kira a Changsha, babban birnin lardin Hunan, ya jaddada bukatar karfafa “kula da cikakken tsarin fitar da manyan ma’adanai masu muhimmanci zuwa kasashen waje.” Taron ya samu halartar jami’ai daga hukumomin gwamnatin tsakiya 10 da yankuna bakwai masu arzikin muhimman ma’adanai, ciki har da jihar Mongoliya ta gida da lardin Jiangxi.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa, “Domin hana fitar da ma’adanai masu muhimmanci ba bisa ka’ida ba, dole ne a fara kula da lamarin daga tushe kuma a karfafa shi a dukkan sassan harkar ma’adanai, da suka hada da hakawa, narkawa, sarrafawa, sufuri, masana’antu, sayarwa, da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp