A game da shakkun da kasashen ketare ke nunawa game da batun bude kofar kasar Sin ga kasashen waje, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, bude kofa ita ce babbar manufar kasar Sin.
Rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya bayyana karara game da inganta bude kofa ga kasashen ketare, inda ya nuna cewa, ya kamata a inganta matakin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari.
Wannan ya kara nuna cikakken kudirin kasar Sin na bude kofa ga ketare bisa babban mataki. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)