Kwanan baya, kafofin watsa labaru na yammacin duniya sun ba da rahoton cewa, yanayin da kasar Sin ke ciki na yaki da annobar COVID-19 zai yi mummunan tasiri ga tsarin masana’antu, da na samar da kayayyaki na kasa da kasa, zai kuma jawo koma bayan tattalin arzikin duniya.
Dangane da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, irin kalaman na da boyayyiyar manufa, kuma sun sabawa gaskiya. Kakakin ya kara da cewa, manufofin rigakafin cutar da kasar Sin ke aiwatarwa, ba wai kawai sun kare rayuka da lafiyar jama’a ba ne, har ma sun rage tasirin da cutar ke kawowa kan ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
A cikin shekaru uku da suka gabata, matsakaicin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kusan kashi 4.5 cikin dari a ko wace shekara, wanda ya zarce na matsakaicin adadin da ake da shi a duniya. Bayan da gwamnatin kasar Sin ta kyautata, tare da daidaita matakan rigakafin da shawo kan cutar, shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da kungiyar WTO, da ta OECD da dai sauransu, gaba daya suna kyautata zaton samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba, a ganinsu kuma, hakan zai taimaka wajen farfado da ci gaban tattalin arzikin duniya.
Dangane da wasu tsirarun kasashe da suka dage kan daukar matakin nuna wariya ga kasar Sin, ba tare da la’akari da gaskiyar kimiyya, da halin da suke ciki na tinkarar annobar ba, kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin ta kara yin kira ga kasashen da abun ya shafa, da su bi hakikanin gaskiya, da kuma tsara matakan kandagarki da suka dace da kimiyya, a maimakon yin amfani da damar wajen yin magudin siyasa da nuna wariya, wanda zai yi mummunan tasiri ga mu’amala a tsakanin mutane, da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)