Kasar Sin ta gabatar da daftarin kudurin dokar da ta shafi shirin raya kasa, ga majalsiar wakilan jama’ar kasar domin tattaunawa da zartar da shi.
A yau Lahadi, kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar Sin (NPC) ya fara taronsa karo na 15 na yini 4, a birnin Beijing.
- Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
- Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas
Dokar na da nufin inganta tsarin tafiyar da dukkan bangarorin da suka shafi tattalin arziki da bayar da cikkakiyar dama ga shirin raya kasa domin ya taka rawar da ya kamata da inganta ci gaba mai inganci da daukaka zamanantar da karfi da tsarin shugabanci na kasar.
Haka kuma za a aiwatar da dukkan abubuwan da aka dade ana yinsu cikin shirin raya kasa a hukumance.
Ana sa ran dokar za ta kara inganta tsare-tsaren da za su tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa da karfafa dacewar manufofin da suka shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da juna. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp