Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta yi tsokaci kan sakamakon zabuka biyu da aka gudanar a yankin Taiwan, inda ta ce, kasarta na adawa da duk wani yunkuri na balle Taiwan daga babban yankin kasar Sin, da yin kira ga kasa da kasa, da kada su dauki duk wani matakin da ka iya hura wutar rikici, na lalata zaman lafiya da tsaron duk duniya. Game da wannan furuci nata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta yaba da ra’ayin na gwamnatin Rasha.
Mao ta ce, hakikanin gaskiya, baya ga Rasha din, akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama a duniya, ciki har da Afirka ta Kudu, da Masar, da Habasha, da Zimbabwe, da kungiyar SCO da kawancen kasashen Larabawa, wadanda suka jaddada matsayinsu na goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da marawa Sin baya wajen kiyaye cikakken ‘yanci da yankinta, da nuna adawa da duk wani yunkurin ware Taiwan, da goyon-bayan babban sha’anin dunkule kasar Sin baki daya.
Jami’ar ta kuma sake nanata cewa, duk wani sauyin yanayi da za’a iya samu a Taiwan, ba zai sauya batu na hakika ba, wato kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, Taiwan wani bangare ne na kasar. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp