Yayin da wasu sassan na ’yan siyasar kasashen yamma ke nuna shakku kan sahihancin niyyar kasar Sin, game da cudanyarta da kasashen Afirka, har ma wasu ke zargin cewa wai Sin na danawa kasashen na Afirka tarkon bashi, a hannu guda, masharhanta da dama na ganin wannan zargi ba shi da tushe ko makama.
Ga misali, karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashen Afirka da dama, wajen samar da manyan ababen more rayuwa masu matukar tasiri ga ci gaban kasashen na Afirka.
Ga misali, a baya bayan nan, masu fashin baki da dama na ci gaba da jinjinawa aikin layin dogo na SGR da ya hada biranen Mombasa da Nairobin kasar Kenya a takaice. Wannan aiki ko shakka babu, ya samar da babbar dama ta bunkasa tattalin arzikin kasar Kenya ta sassa da dama.
Bayan fara aiki da wannan layin dogo na SGR a shekarar 2017, aikin ya samar da tarin guraben ayyukan yi, ya kuma bunkasa sashen sarrafa hajojin masanaantun kasar. Kaza lika aikin ya raya harkar kasuwanci tsakanin Kenya da sauran kasashen duniya. Baya ga inganta fannin fiton manyan kayayyaki ta tashar jiragen ruwan kasar.
Bugu da kari, bisa hasashen masana, layin dogo na SGR zai rika samarwa mizanin awon tattalin arzikin na GDPn kasar Kenya kaso 2 zuwa 3 bisa dari a duk shekara.
Layin dogo na SGR mai tsawon kilomita 480, babban aikin more rayuwa ne da aka aiwatar karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar.
Irin wadannan ayyuka muhimmai da suka kasance jigon hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka, na nuni ga irin kyakkyawar abota dake tsakanin Sin da ’yan uwanta na kasashe masu tasowa, kuma hakan na tabbatar da ingancin alakar sassan biyu cikin tsawon lokaci, don haka ba zai yiwu, wani ya iya cimma nasarar bata alakar wadannan sassa da suka riga suka amincewa da juna ba!