Bisa labarin da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayar a shafinta na yanar gizo, an ce, bisa dokoki da mizani masu alaka na babban yankin kasar, daga yau Laraba 3 ga wata, an dakatar da shigar da lemon tanjarin da dangoginsa, da danyen kifi mai tsayi nau’in “hairtail” da ake samu a teku, da daskarren kifi nau’in “Japanese Jack Mackerel” daga yankin Taiwan.
Haka kuma, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya nuna cewa, bisa tanade-tanaden da ke cikin dokoki masu alaka da hakan, an dakatar da sayar da yashi irin na “Natural sand” zuwa yankin na Taiwan, tun daga yau Laraba 3 ga watan Agusta. (Tasallah Yuan)
Talla