• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Tsibiran Pacific Ba Za Su Zamo Makamin Amurka Na Aiwatar Da Siyasar Yanki Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Pacific

A ranar Alhamis, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya jagoranci taron ministocin harkokin waje na kungiyar kawancen yankin Pacific ko PBP a takaice, a yayin babban taron MDD.

Inda a lokacin ya yi ikirarin cewa, Amurka za ta himmatu sosai, ga bunkasa yankin tekun Pacifik, tare da hada kai tare da kasashen shiyyar wajen magance sauyin yanayi, da karfafa muhimman ababen more rayuwa da dai sauransu.

  • Dakarun Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya

Kasashen waje sun yi imanin cewa, hakan tamkar share fage ne ga “Taron Amurka da Tsibiran Pacific” karo na farko, wanda za a gudanar a birnin Washington a karshen watan Satumbar nan.

A watan Yunin bana ne aka kafa kungiyar da ake kira PBP, kuma wasu kafofin yada labaran Amurka sun yi nuni da cewa, manufar PBP ita ce daidaita tasirin da kasar Sin ke da shi a yankin kudancin tekun Pacifik.

Bisa yanayin siyasar bangaranci ta Amurka, an yi watsi da kudancin Pacific cikin dogon lokaci, amma ko me ya sa a yanzu ake mayar da hankali a kan yankin? ‘Dan majalisar wakilan Amurka Steve Chabot, na da ra’ayin cewa, yarjejeniyar tsaron da aka kulla tsakanin Sin da tsibirin Solomon a farkon wannan shekara ta bukaci Amurka da ta aiwatar da matakai cikin gaggawa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Muddin burin Amurka ba ya da tsarki, abu ne mai wuya kasashen tsibiran Pacific su amince da ita. Firayim ministan kasar Fiji Frank Bainimarama ya taba cewa, “Babban abin da ke damun mu, ba wai batun siyasar bangaranci ba ne, mun fi damuwa da batun sauyin yanayi.”

A nasa bangare kuwa, wani jami’in bincike a cibiyar nazari ta Lowy dake kasar Australiya Mihai Sora, cewa ya yi “Shugabannin yankin tekun Pacific suna kyamar a yi amfani da su, a matsayin makamin aiwatar da siyasar yanki”.

A sa’i daya kuma, a ko da yaushe, Amurka tana kasancewa “Babban hadari mai saukar dan yayyafi” a fannin ba da agaji ga kasashen waje, lamarin da ya sanya kasashen dake tsibiran tekun Pacifik, ke nuna shakku kan alkawuran da ta dauka. (Mai fassara: Bilkisu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
2023: Mace 1 Ce Ta Fito Takarar Shugaban Kasa Da Wasu 380 A Kujerun Majalisar Tarayya – INEC

Yayin Da Ake Dab Da Fara Yakin Neman Zaben 2023, Ga Abubuwan Da INEC Ta Gargadi 'Yan Takara A Kansu

LABARAI MASU NASABA

Pacific

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.