Ana wawushe albarkatun Kasa da ma’adinai, ana kwace ’yancin mallakar kasa, ana zaluntar mutane. Wannan ita ce mummunar fahimta da da’awar da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke yadawa game da shirin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ko BRI a takaice. A wajensu, BRI na nufin “farauta” da “tsangwama.”
An ce wanzami ba ya son jarfa, a hakikanin gaskiya wannan kage da kasashen yamma suka yiwa shirin BRI da nufin muzgunawa kasar Sin na bayyana ainihin illoli wadanda suka hada da mamaya, katsalandan, tsangwama da babakeren da Amurka da kawayenta na yamma suka yiwa kasashen Afirka ne.
- Ganawa Da Xi Jinping: Ina Godiya Gare Shi Bisa Cimma Burina
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Halarci Bikin Bude Taron BRF
Bari mu kawo wasu misalai sa’annan mu kwatanta bangarorin biyu, za mu fahimci wace kasa ce ke “farautar Afirka da tsangwama mata” tsakanin kasar Sin da Amurka da kawayenta na yamma. Kasar Amurka ta kafa sansanonin sojoji 29 a nahiyar Afirka yayin da kasar Sin take da daya a Djibouti. Amma duk da haka Amurka na ikirarin cewa Sin ce ke yin katsalandan a nahiyar.
Gaskiya ne cewa kasar Sin na gina layin dogo a duk fadin Afirka wanda Joe Biden shugaban ƙasar Amurka ya yi mafarkin cewa Amurka za ta gina, a maimakon haka, shugabannin na Amurka sai tofin Allah wadai da ayyukan Sinawa a Afirka suke ke yi, alhalin a duk ziyararsu a Afirka alal akalli sai sun sauka a wani filin jirgin saman Afirka da Sin ta gina, su kuma shiga cikin gari a kan wata babbar hanyar da kasar Sin ta shimfida. Wannan shi ne ake ce ma munafurcin dodo ya kan ci mai shi.
To wai shin mene ne shisshigi kuma mene ne ci gaba? Kasar Sin ta shiga Afirka lungu da sako tana taimakawa wajen gina ababen more rayuwa da Turawan mulkin mallaka ba su taba ginawa ba, da kuma taimakawa wajen gina makomar tattalin arziki mai cin gashin kanta bayan mulkin mallaka, wanda kasashen yammacin duniya suka yi duk mai yiwuwa don hanawa.
Kasar Sin ba ta bautar da kowa a Afirka ba kuma kasar Sin ba ta mamaye ko’ina a Afirka ba. Amma babu wata kasa a nahiyar Afirka da kasashen yamma ba su debi magabatanmu a matsayin bayi zuwa kasashensu suka bautar da su ba. Kana, babu wani inchin murabba’i na kasa da mulkin mallakar yamma bai mamaye ba.
Wane ne ya taba kashe shugabannin kasashen Afirka? Kasar Sin ba ta yi juyin mulki ba a Afirka. Hasali ma, Sin ba ta tsoma baki a harkar shugabancin kasashen waje, wannan ka’ida ce ta Sin. Ba sai na tunashe mu ta’adin da kasar Amurka ta aikata a kasar Libya zuwa Timbuktu, ko kasar Laberiya zuwa Congo ba.
Kasar Sin ba ta taba goyon bayan wariyar launin fata a Rhodesia da Afirka ta Kudu ba. Sabanin haka, kasar Sin ta goyi bayan gwagwarmayar ‘yanci a dukkan bangarorin biyu. Yamma ce ta rura wutar fitinar wariyar launin fata da ta samu tushe a tarihin kasashen biyu.
Ba kasar Sin ce ta karya farashin Uranium na Nijar zuwa wajen Yuro 0.1 kan ko wane kilogiram ba, a lokacin da farashin a kasuwa ya kai wajen Yuro 25 kan kowane kilogiram na Uranium daga Nijar. Har ila yau, wannan shi ma makircin yamma ne.
Shirin shawarar “ziri daya da hanya daya” na kasar Sin yana shimfida hanyoyin mota, layin dogo da habaka sufurin jiragen sama, da gina makarantu, asibitoci, jami’o’i da makarantun kananan yara.
Su kuma kasashen yamma na totse jinin ’yan Afirka kamar yadda suka yi shekaru aru-aru da suka gabata, yayin da kasar Sin ke kawo bege. Wannan shi ne bambanci tsakanin Sin da kasashen Yamma. (Muhammed Yahaya)