Shirin tallafin ilimi na PLANE, wanda ofishin FCDO na Burtaniya ke ɗaukar nauyi, ya bayyana cewa kusan kashi 25% na makarantun firamare a Kano na da malami ɗaya ne kawai wanda ke koyarwa a duk aji.
Wannan bayanin ya fito ne yayin wani taron gabatar da sakamakon bincike kan ingancin karatu da aka gudanar a ƙananan hukumomin da PLANE ke aiki a jihar.
- Gwamnatin Kano Za Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Hausa – Mataimakin Gwamnan Kano
- Gwamnatin Kano Ta Miƙa Yara 76 Da Aka Kama Yayin Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
Binciken ya nuna cewa kowane malami yana koyar da yara kusan 131, wanda ya ninka sau hudu bisa ga ƙa’idar UNESCO ta 35:1. Haka kuma, an gano cewa kaso 79% na yara a ajin Kano ba su da kayan aiki kamar fensir da littattafan rubutu. Duk da haka, an samu ci gaba a ɓangaren karatun harshen Turanci da lissafi a makarantun da ake tallafawa.
Me bayar da shawarar a ɓarin FCDO, Joseph Wales, ya yaba da nasarorin da aka samu, yana mai cewa za a yi amfani da irin wannan tsarin don ƙarfafa haɗin kai a matakin al’umma, da ƙananan hukumomi, da Jiha don inganta ilimi.
Wakilin PLANE, Sam Achimugu, ya bayyana cewa suna aiki tare da gwamnati don tabbatar da cewa yara sun fi ƙwarewa a karatun harshe da lissafi a duk jihar.
Sakatariyar hukumar SUBEB, Amina Umar, ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta fara ɗaukar matakan gyara, ciki har da tabbatar da rarraba malamai daga yankunan birni zuwa karkara don magance rashin malamai. Ta kuma yi kira ga shugabannin LGA da su naɗa shugabannin ilimi masu kwarewa domin magance matsalolin rashin halartar malamai da ɗalibai.
Taron ya haɗa wakilai daga ma’aikatar Ilimi, da SUBEB, da FCDO, da sauran masu ruwa da tsaki don tsara dabarun ci gaba.