Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da samun gagarumar nasara a fannin ilimi, inda sama da kashi 67 cikin 100 na dalibanta suka samu sakamako mai daraja ta biyar (C5) zuwa sama a jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE).
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Muhammad Sani Bello ne ya bayyana haka a taron kwana daya da hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar (KSSQA) ta shirya mai taken “Quality Assurance in Education: Summit for Best Practices”.
- Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo
- Karin Farashin Man Fetur: Ko Tinubu Zai Saurari Muryar Talaka?
Da yake zantawa da manema labarai, Farfesa Bello ya ce, wannan gagarumar nasara da aka samu, ta nuna irin hoɓɓasa da gwamnatin Gwamna Uba Sani ke yi a ɓangaren ilimi, da nufin daukaka darajar ilimi a jihar.
Farfesa Bello ya yi nuni da cewa, “Kaduna ta himmatu wajen ganin cewa, ba wai kawai samun ilimi ba, har ma da tabbatar da dalibai sun kammala karatunsu da sakamako mai kyau. Mun riga mun ga gagarumar nasara, kuma muna fata wannan nasarar za ta ci gaba”
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa, tsarin ilimin jihar nan ba da jimawa ba zai zama na daya a Nijeriya wajen bayar da ilimi. Kwamishinan ya bukaci sauran hukumomi da su yi koyi da hukumar tabbatar da ingancin ilimi wajen aiwatar da dabarun kula da ingancin ilimi.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Farfesa Usman Abubakar Zaria, babban darakta a hukumar KSSQA, ya bayyana matakai daban-daban da aka dauka na karfafa matakan ilimi a makarantun gwamnati da masu zaman kansu. Ya jaddada cewa, dole ne makarantu masu zaman kansu su bi ka’idojin tabbatar da ingancin ilimi a jihar.
“Daya daga cikin manyan nasarorin da muka samu a karkashin Gwamna Uba Sani shi ne, daukakar darajarmu a wurin samun sakamakon jarabawar kammala sakandire ta WAEC daga kashi 54 zuwa kashi 67 cikin 100, kuma darajarmu ta tashi daga na 10 zuwa na 7 a fadin kasar nan. Mun kuma bullo da ingantattun tsarin tantance jabun sakamako ta hanyar amfani da na’urar (QR code) da kuma fitar da sabbin fasahohi, kamar na’urorin kwamfuta, don inganta koyo,” in ji Farfesa Zaria.
Da yake jawabi a kan matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu sassan jihar, Farfesa Zaria, ya ce, duk da cewa a baya rashin tsaro ya yi tasiri wajen hana yara shiga makarantu, amma a baya-bayan nan an samu ci gaba a fannin tsaro a fadin jihar, wanda a halin yanzu kananan yara da suka shiga makarantun firamare sun kai kusan miliyan 1.8, wanda a shekarar baya aka samu kimanin yara miliyan 1.7