Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce, sama da yara kashi 70 cikin dari a Nijeriya ba su samun Nonon Shayarwa.
Darakta mai cikakken iko na UNICEF, Catherine Russell da darakta-janar na Tedros Ghebreyesus su ne suka shaida hakan a sanarwar hadin guiwa da suka fitar kan makon Shayarwa ta duniya na 2022, sun kara da cewa rikice-rikicen duniya na kara barazana ga harkokin lafiya da samar da abinci mai gini jiki ga jarirai da yara kanana, kuma shayar da jariri Nonon uwa a farkon rayuwarsa na da matukar muhimmanci fiye da kowani lokaci.
- CJTF Ta Cafke Wata Mata Kan Safarar Almajirai 2 Da Yarinya A Borno
- Manyan Kasuwannin Da Aka Fi Samun Goruba A Nijeriya
Kan bikin na wannan shekarar, UNICEF da WHO na kira ga gwamnatoci da su kara himma wajen samar da kudade domin karewa da inganta harkokin shayar da jarirai ta hanyar tsare-tsaren da shirye-shirye, musamman ga iyalan da suke fama da talauci da fatara.
Kungiyoyin sun ce halin da lamarin shayar da jarirai ke ciki a Nijeriya abun damuwa ne matuka don haka ne suka nemi gwamnatocin da kara himma wajen shawo kan matsalolin da ake fama da su wajen shayar da jarirai musamman Nonon uwa zallah.
Wakilinmu ya nakalto cewa matsalolin rayuwa da na tattalin arziki na daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta wajen samun abinci mai inganci da uwa za ta ci don shayar da jariranta, kana hakan na janyo nakasu ga samun abinci mai gina jiki ga yara kanana.