Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Nijeriya a taron shekara-shekara na tattalin arziƙi na Duniya (WEF) na 2025 da za a gudanar a Davos, Switzerland.
A wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, an bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar zai haɗu da shugabannin duniya, da manyan ‘yan kasuwa, da wakilan abokan ci gaba don tattauna halin da tattalin arziƙin duniya ke ciki da hanyoyin da za a inganta shi.
- Shettima Ya Yaba Wa BUK Kan Bai Wa Dalibai Guraben Karatu Cikin Adalci
- Ku Yabi Nasararmu, Ku Soki Kura-kuranmu – Kiran Shettima Ga ‘Yan Jarida
Shettima zai halarci tattaunawa da taruka daban-daban ciki har da taron da Bankin Ci Gaban Afrika (AfDB) ya shirya, mai taken “Taswirar Haɗin Gwuiwar Jari Don Kasuwannin Ci gaba na Afrika”. Haka kuma, za a tattauna batun “Kasuwancin Zamani a Matsayin Jigon Ci Gaba a Afrika” don tallafa wa yarjejeniyar AfCFTA ta fannin kasuwancin Zamani.
Za kuma ya halarci tattaunawa kan “Manyan Barazanar da ke fuskantar Duniya na 2025” da sauran mahimman abubuwan da suka shafi tattalin arziki da ci gaban Afrika. Ana sa ran dawowar Shettima bayan kammala ayyukansa a Davos tare da wasu manyan jami’an gwamnati.