Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, ya ce, rukunin farko na daliban da za su shiga makarantun kasashen waje za su fara tafiya daga watan Satumba.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mukaddashin sakataren yada labaran gwamnan, Hisham Habib, ya fitar a Kano ranar Asabar.
- Gwamnatin Kano Za Ta Bincike Dakatar Da Albashin Ma’aikatan Kano
- Ban Yi Nadamar Rusau A Kano Ba -Gwamnan Kano
Yusuf ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, da ‘yan majalisar masarautar Bichi a lokacin bikin Sallah.
Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na baiwa fannin ilimi fifiko.
Ya kuma bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shiryen sake bude cibiyoyin ilimi 20 da gwamnatin da ta shude ta rufe.
Yusuf ya godewa sarkin tare da rawar da sarakunan suka taka a matsayin masu kula da al’adu da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba.
Tun da farko, Sarkin Bichi, ya yi kira da a samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa da farfado da noman itatuwa da samar da ruwan sha a jihar.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da yanayin da zai taimaka wa masu zuba jari don ci gaban jihar.
Bayero ya yabawa gwamnan bisa nada dan masarautar Dr. Baffa Bichi a matsayin sakataren gwamnatin jihar. (NAN)