‘Yan bindiga dadi sun mamayi majami’ar Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke jihar Ogun, inda suka kashe wani Fasto da sace wasu masu Ibada.
Lamarin ya faru a Abule-Ori da ke karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar a karshen makon nan.
- Sulhu Da ‘Yan bindiga Ne Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Yerima
- Masu Garkuwa Sun Sace Babban Limami A Ondo
Kwamandan rundunar So-Safe Corps a jihar Ogun, Soji Ganzallo, ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar ranar Lahadi.
Ya ce, jami’ansa sun ceto mutum bakwai daga cikin mambobin cocin tare da kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen a yayin aikin ceton da suka kaddamar.
A sanarwar da daraktan yada labarai na So-Safe, Moruf Yusuf ya fitar, ya rawaito Ganzallo na cewa lamarin ya faru da misalin karfe 12am na ranar Asabar 1 ga watan Yuli.
Ganzallo ya kara da cewa, cikin hanzari bayan samun labarin harin suka tura jami’ansu da zimmar su ceto wadanda sa aka yi garkuwa da su cikin hanzari.