Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, ya bayyana cewar gawurtaccen dan bindiga Bello Turji da ya shahara wajen sace mutane, ya saduda ya rungumi zaman lafiya kana ya daina kai hare-hare kan jama’a a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi.
Hassan, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan tsaro a Gusau babban birnin jihar, wanda kungiyar daliban Jami’ar Madina suka shirya, inda ya ce, shi Bello Turji a bisa radin kansa da kashin kansa ya amince wajen kawo zaman lafiya a kananan hukumomin uku, inda suka kasance wuraren boyar masu garkuwa da mutane da ke kai hare-hare ga jama’a a Jihar Zamfara da shiyyar Arewa Maso Yamma.
- Sojoji Sun Dakile Yunkurin Kafa Sansanin ‘Yan Bindiga A Jihar Neja
- El-Rufa’i Ne Silar Matsalar Tsaro A Kaduna – Shehu Sani
A cewar mataimakin gwamnan, Sanata Nasiha, sama da makonni biyar da suka wuce ba a samu fada tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi ba sakamakon rungumar sulhun da ya kawo zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.
Ya bayyana cewar Bello Turji yanzu haka da kansa yake yakar sauran ‘yan bindigar da suka ki rungumar zaman lafiya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A cewarsa, gwamnan Jihar Bello Muhammad, ya kafa kwamiti wanda kuma shi da kansa ke jagoranta sun zauna da ‘yan bindiga da mutane tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau ta Gusau da karamar hukumar Maru, inda suka tattauna kan zaman lafiya tare da nemansu da su daina kai hare-hare ga jama’a.
A cewar Nasiha, gwamna Bello Mohammed, ya umarci cewa dukkanin wuraren kiwo, labi da mashayar dabbobi da wasu kadarorin da aka kwace sakamakon rikici tsakaninsu da Hausawa da a gaggauta maida musu domin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Hassan Nasiha, ya kara da cewa Fulanin suna son gwamnati ta samar musu da taki, a kuma saki Fulanin da suke tsare a gidajen yarin jihar kana a gina wa ‘ya’yansu makarantu.
A cewarsa, samar musu da wadannan bukatun zai taimaka wajen rage musu sha’awar shiga harkokin garkuwa da mutane sakamakon karancin ilimi da ke jefa su cikin wannan abun.