Babban shugaban gamayyar kungiyoyin kasuwannin al’ummar Hausawa mazauna Jihar Legas, Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam Dallatun Abeokuta ta Jihar Ogun.
Kuma Shugaban kasuwar mile12 intanashinal market a Legas ya bayyana cewar hakika a halin yanzu shi da sauran shugabannin bangarorin kasuwar ta mile12 Intanashinal maket da ke cikin birnin Legas suna kara samun nasarori a wajen gudanar da harkokin jagorancin kasuwar ta mile12 da kewayan ta baki daya.
- ‘Muna Kira A Samar Da Jami’an Tsaro Na Yankin Arewacin Nijeriya’
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Shehu Samfam ya yi wannan furuci ne a Kano a satin daya gabata jim kadan bayan kammala taron gudanar da addu’ar daurin auran ‘ya’yan Alhaji Umar Dangara wanda ya gudana a garin Sarina ta karamar hukumar Garko da ke cikin Jihar Kano.
A taron an gudanar da addu’o’in daurin auran wanda ya kunshi dukkan shugabannin bangarorin kasuwar ta mile12 da sauran manyan baki wadanda suka fito daga sassa daban-daban na jihohin kasar nan baki daya.
Bayan kammala taron gudanar da addu’o’in daurin auran ne Alhaji Shehu Usman jibirin Samfam ya cigaba da yi wa Alhaji Umar Dangara da sauran ‘yan kasuwar wadanda suka gudanar da irin wannan taro na gudanar da mahimmancin addu’o’i na musamman fatan alheri a game da samun damar da Allah ya basu ta gabatar da wannan al’amari sannan kuma ya ci gaba da yin tsokaci a bisa kan nasarorin da yake ganin kasuwar ta mile12 ta samu a karkashin jagorancinsa da sauran kasuwannin Hausawa mazauna cikin garin Legas.
Ya ci gaba da cewa na farko dai kasuwar ta mile12 ta samu hadin kawunan shugabannin bangarorin kasuwar dana sauran ‘yan, kasuwa masu gudanar da harkokin kasuwanci a cikin kasuwar ta mile12 sannan kuma ya ce ta samu ci gaba ta fannin ayyuka.
Ya ce saboda idan kakai shekaru biyar zuwa goma baka shiga kasuwar ta mile12 ba idan ka shigeta a halin yanzu zaka ga abubuwan cigaba na bam mamaki.