Ɗan wasan gaban Eintracht Frankfurt, ɗan asalin ƙasar Masar, Omar Marmoush, ya amince da tayin da Manchester City ta yi masa na komawa Ingila domin taka leda.
Marmoush na ɗaya daga cikin matasan ‘yan wasa da suke haskakawa a halin yanzu, inda manyan ƙungiyoyin ƙwallon kafa ke zawarcinsa domin ya koma ƙungiyoyinsu.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Babban Layin Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Lalace Karon Farko A 2025
- Gobara Ta Yi Ɓarna A Kwara, Shaguna 7 Sun Ƙone
Ana hasashen Marmoush zai koma Etihad a wannan watan na Janairu, yayin da kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ke ci a Turai.
Rahotanni sun nuna cewa Manchester City za ta biya kimanin Yuro miliyan 60 domin ɗaukar ɗan wasan gaban na ƙasar Masar.