Bisa yawaitar yankewar kebul-kebul na cikin teku a ‘yan kwanakin baya da ya janyo katsewa da cikas ga ayyukan internet a Nijeriya da ma wasu sassan kasashen yammacin Afrika yanzu haka na bukatar makonni shida ko takwas kafin a iya gyarawa da cikakken karfin network zai dawo kamar yadda yake, a cewar bayanin da MainOne ta fitar.
LEADERSHIP ta labarto cewa a ranar Alhamis 14 ga watan Maris na 2024 al’umma sun fuskaci matsalolin yankewar karfin networks a kasashe 12 na Afrika ciki har da Nijeriya.
- Kisan Okuama: Baƙin Cikin Da Ke Tattare Da Labarin
- An Gabatar Da Rahoton Binciken Kamfanonin Sin Game Da Halinsu Na Zuba Jari a Ketare a 2023
Wadanda matsalar yankewar kebul din cikin tekun ya shafa sun hada da na West Africa Cable System (WACS), Africa Coast to Europe (ACE), MainOne, da kuma SAT3, wanda suka yi mummunar tasiri wajen kawo cikas ga lamuran data da kuma kamfanonin sadarwa a kasashe da dama na yammacin Afrika, musamman wadanda suka fi fuskantar matsalar ma su ne Nijeriya, Ghana, Senegal da kasar Kod-debuwa da lamarin ya janyo cikas da katsewar sabis din yanar gizo kuma ya shafi bangarorin tattalin arziki.
Nijeriya dai na cigaba da kirga maguden kudade na biliyoyi da take asararsu sakamakon lalacewar manyan igiyoyin kebul da ke karkashin tekuna musamman kebul din da ke Bahar Maliya da na gabar tekun yammacin Afrika. A misali, NetBlocks da ke sanya ido kan tsaron yanar gizo da yadda ake gudanar da lamuran internet, ya yi kiyasin cewa Nijeriya ta yi asarar naira biliyan 273 a cikin kwanaki hudu tsakanin ranar 14 ga watan Maris zuwa 17 ga watan Maris.
Kamfanin fasahar zamanin wanda ya bada bayanin tsare-tsaren gyaran a ranar Litinin, an kuma jero ranakun da za a bi wajen gyaran tare da cewa tunin aka fara jibge wasu kayan da suka shafi na gyara.
Kamfanin ya ce domin gyara manyan kebul-kebul dinsa guda hudu, yanzu haka na aikin hadin guiwa da abokan hulda wajen ganin an cimma nasara, “Muna da kwarin guiwar gyaranmu na igiyoyin sadarwarmu za su yi nasara kuma karfin sabis dinmu zai dawo yadda ya dace.”
Domin dakile faruwar irin wannan a nan gaba a Afrika baki daya, shugaban WIOCC, Chris Wood, ya ce gyaran zai iya lakume wa Afrika sama da dala biliyan daya wajen shimfida sabbin igiyoyin internet daga Afrika ta kudu zuwa Europe, da zai hada kasashe da dama ciki har da Nijeriya.
“Akwai tsada sosai a ina gina sabun kebul daga Afrika ta kudu zuwa Turai, da zai hada kasashe da daman gaske. A kalla zai iya cinye dala biliyan 1, wanda ya yi yawa sosai. Don haka ba abu ne mai sauki ba. Zai yi nauyi wa mutum ya biya wannan dalolin, ammai akwai bukatar ganin alfanunsa idan an cire kudi, sai dai zai dauki tsawon lokaci kafin a iya tsara wadannan igiyoyin.”
Ma’aikata Ta Samar Da Shafin Yanar Gizo Domin Zamanantar Da Ayyukanta
A yunkurin ma’aikatar gwamnatin tarayya na zamantar da ayyuka da tafiya daidai da zamani, ma’aikatar gidaje da tsara birane ta gwamnatin tarayya ta samar da wani shafin yanar gizo da ya kasance turaka da zai ke saukaka tafiyar da ayyukanta.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar Badamasi Salisu Haiba ya fitar, ya ce turakar yanar gizon shine irinsa na farko da ma’aikatar ta yi tun lokacin da tsame ma’aikatar daga ma’aikatar ayyuka da gidaje yanzu shafin shi ne www.fmhud.gob.ng.
Da ya ke kaddamar da shafin, babban sakatare a ma’aikatar, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya jinjina wa kokarin sashin fasahar zamani na ma’aikatar (ICT) bisa inganta matakin samar da internet mai karfi, a cewarsa, lamarin wani mataki ne mai kyau na tafiya daidai da zamani a lamuran da suka shafi hidimar aiki, wanda a cewarsa na daga daga cikin muhimman ginshiki da tsare-tsaren da dabarbarun ma’aikatar kula da ma’aikata ta gwamnatin tarayya ta sanya a gaba (FCSSIP 25).
“Fasahar zamani wani mataki ne da ake kokarin dauka na inganta ayyukan gwamnati da shi, don haka wannan kaddamarwar da ma’aikatar ta yi na sashin yanar gizo babban cigaba ne kuma abun murna ne,” ya shaida.
Da yake umartar dukkanin rassa da sashi-sashi da suke tura aikace-aikacensu ga sashin fasahar zamani (ICT) na ma’aikatar domin kwaskwarima da daurawa a shafin yanar gizon kai tsaye, babban sakataren ya kuma sanar da karin cigaba na cewa an kirkiri turakar email a hukumance ga kowani ma’aikacin ma’aikatar, ya ce, hakan zai taimaka wajen kyautata aiki da saukaka aiki hadi da wanzar da komai cikin gaskiya.
Tun da farko, daraktan sashin fasahar zamani, Marcus Amiolemen, ya ce, “Yanzu zamani ne na yanar gizo, kowace kungiya ko ma’aikaar da ta kasa mallakar shafin yanar gizo ba za ta samu nasarar cimma muhimman nasarori ba.
“Wannan shafin da muka samar zai kasance dandamali na baje ayyuka da shirye-shiryen ma’aikatar ga duniya baki daya, shafin na da saukin shiga,” ya shaida.