Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirinta na gudanar da jarabawar tantancewa ga dukkan shugabanni da mataimakan shugabanni, da malaman makarantun sakandire na jihar.
Za a shirya jarrabawar ne da nufin taimaka wa gwamnati wajen sake nada mukamai da kuma tabbatar da matakin da ya dace ga shugabancin makarantu, da inganta kwazo da ingantaccen jagoranci a makarantu.
- Yawan Jarin Waje Na Kai Tsaye Da Sin Ta Zuba A Bara Ya Kai Dala Biliyan 177.29
- Jami’an ‘Yansanda 5 Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota A Kano
Kwamishiniyar ilimin farko da sakandire a jihar, Zainab Musawa ce ta bayyana hakan a Katsina yayin da take yi wa manema labarai karin haske kan yadda daliban jihar suka samu sakamako mai kyau bayan kammala jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) na shekarar 2024.
Musawa ta bayyana cewa, ma’aikatar ta kuma shirya sake dawo da azuzuwan bada horo na tilas ga duk daliban da suka kusa kammala makarantar sakandire domin kara musu kaimi musamman a fannin Lissafi da Turanci.
Yayin da take jaddada kwazon dalibai a jarabawar NECO, kwamishiniyar ta ce, jihar ta zo ta shida a yawan daliban da suka fita da (credit 5) zuwa sama da haka, da suka hada da Lissafi da Ingilishi, wanda ta bayyana a matsayin babban nasara.
Ta kara da cewa, wannan gagarumar nasara da daliban suka yi, nuni ne na gaskiya da irin jajircewar da gwamnati ta yi wajen kawo sauyi a fannin ilimi, da samar da kayayyakin koyarwa, da kayayyakin aiki, da kuma daukar fiye da malamai 7,000 aiki tun lokacin da gwamnati mai ci a jihar ta zo.