Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya yi alkawarin gyara shagunan da suka lalace a sakamakon ibtila’in Gobara da ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako da ke babbar kasuwar Muda Lawan a jihar.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin samar musu da agajin gaggawa.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’a da daddare ne muka wallafa labarin tashin gobarar a kasuwar na ‘yan Katako, lamarin da ya kai manyan shaguna cike da kaya har 12 suka kone kurmus tare da yin asarar miliyoyin naira.
A ziyarar duba barnar da gobarar ta yi, gwamna Bala Muhammad, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan goma kari akan alkawarin gyara shagunan da suka lalace.
Kazalika, gwamnan ya kuma sake yin alkawarin cewa zai samar da na’urar rarraba wutar lantarki a kasuwar don kyautata karfin wutar lantarki a kasuwar domin habaka hada-hadar kasuwanci.
Da ya ke umartar hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta kiyasce asarar da aka yi.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah kare faruwar hakan a nan gaba tare da jajanta wa wadanda shagunansu ya kone.
A jawabinsa na godiya a madadin wadanda ibtila’in ya shafa, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Muda Lawal, Alhaji Bala Mai Kaji, ya nuna godiyarsu bisa nuna damuwa da kauna da gwamnan ya nuna musu.