Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci tattaunawar tawagar wakilan jama’a ta Jiangsu, a gun zama na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 a watan Maris na shekarar 2024, ya yi bayani bayan da ya saurari sabon ci gaban da kauyen Yonglian na birnin Suzhou dake lardin Jiangsu ya samu na neman cimma burin samun wadata tare, inda ya ce yayin da ake kokarin bin hanyar neman samun ci gaban kauyuka da samun wadata tare, kauyen Yonglian ya zama a kan gaba, ya kamata a nemi hanya mai dacewa, da sa kaimi ga samun wadata, tare da kuma samun zamanintarwa iri ta kasar Sin.
Don samun wadata tare, an fi dora muhimmanci ga kauyuka. Ya kamata kauyuka su san yanayin da suke ciki, da yin kokarin neman hanyoyin samun ci gaba masu dacewa bisa yanayinsu.
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Ranar Tunawa Da Mazan Jiya: Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Inganta Rayuwar Iyalan Jaruman Da Suka Rasu
Sabon zaman rayuwa a kauye mai kudin shiga fiye da Yuan biliyan 100
Shugaba Xi na kasar Sin ya ce, burin samun wadata tare, buri ne a tsakanin dukkan jama’ar kasar Sin, kana buri ne dake shafar tattalin arziki da kuma zaman yau da kullum baki daya.
Kauyen Yonglian kauye ne da aka gina shi a kan gefen kogin Yangtze, wanda ya taba zama kauye mafi talauci a wannan yanki. A shekaru 80 na karni na 20, bisa manufar bude kofar kasar Sin ga sauran sassan duniya da yin kwaskwarima kan tattalin arziki a duk fadin kasar Sin, an kafa wani kamfanin samar da karfe a wannan kauye, kamfanin ya kuma samu babban ci gaba, har ma ya zama kamfanin Yonggang, wanda ke cikin manyan kamfanonin kasar Sin 500 masu zaman kansu. A shekarar 1998 da kuma ta 2000, kamfanin Yonggang ya canja tsarinsa sau biyu, kuma ya baiwa kauyen Yonglian kashi 25 cikin dari na hannun jarinsa.
A shekarar 2005, Wu Huifang wanda ya yi ritaya daga rundunar soja, ya koma kauyen ya zama shugaban sashen kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin na kauyen, kuma ya jagoranci mazauna kauyen wajen ci gaba da raya kauyen tare. A cikin wasu shekaru, an gina hanyoyin motoci, da gidaje, da kasuwa ta zamani, da kantuna, da asibitoci, da makarantu da sauransu a kauyen, kuma a yanzu kauyen Yonglian ya zama wani kauye mai ci gaban tattalin arziki da jin dadin zaman rayuwa.
Amma Wu Huifang, ya gano karin lamura marasa kyau a kauyen bayan da kauyen ya samu ci gaba. Ya ce ban da kawo karin kudin shiga ga mazauna kauyen, ya kamata a kawo sabon yanayin zaman rayuwa na jin dadi gare su.
Don haka, an fitar da lambar yabo ta iyali mafiya kwazo a kauyen, da sa kaimi ga mazauna kauyen su rika kiyaye dabi’a, da koyon ilmi da kuma bude idanunsu. Kana an gina wurin yawon shakatawa, da gidajen ajiye littattafai, da cibiyoyin bada hidima da sauransu, inda mazauna kauyen suke iya shiga ba tare da biyan kudi ba. Kaza lika, an gayyaci tawagogin yada al’adu na kasar Sin, da na kasashen waje zuwa kauyen don gabatar da shirye-shiryensu, da kafa kungiyoyin rawa da dragon, da na ganga a kauyen da sauransu.
A shekarar 2023, jimillar kudin shiga da aka samu daga masana’antu da aikin noma a kauyen Yonglian ta kai kudin Sin Yuan biliyan 161.6, kana kudin shiga na kowane mazauni kauyen ya kai dubu 73. Haka zalika, an baiwa kauyen Yonglian lambar yabo ta kauye mafi samun ci gaba a dukkan fannoni na kasar Sin, inda a karo 6 a jere kauyen ya lashe wannan lambar yabo, kuma an kara kyautata zaman rayuwar mazauna kauyen a dukkan fannoni.
Wu Huifang ya ce, samun wadata a fannin tattalin arziki tamkar cimma rabin nasara kawai, ya kamata a tuna da maganar shugaba Xi, wato cimma burin samun wadata tare a dukkan fannoni.
Daga kauyen rairayi zuwa kauye mai arziki
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, yayin da ake kokarin neman samun wadata tare, ya kamata bangaren da ya riga ya samu wadata ya taimakawa duk inda suke fama da talauci wajen samun wadata tare.
An shiga lokacin girbin borkono a gonakin aikin noma na zamani na Shuifahaohai, na kauyen Hongde na garin Hongsibu dake birnin Wuzhong na jihar Ningxia, wanda shi ne aikin hadin gwiwa a tsakanin gabashi da yammacin yankin. Bayan kyautata tsarin aikin a shekarar bara, wani mazauni kauyen Guangcai, Liu Sisheng ya sauya shekarsa daga ma’aikaci zuwa mai kula da gonaki.
Liu Sisheng ya bayyana cewa, an samu kayayyakin aikin noma daga gabashin yankin, kana an tura masu kwarewar fasaha zuwa wurin, inda shi ma yake kula da harkokin wurin. Kana an sayar da ’ya’yan itatuwa da kayan lambu zuwa biranen gabashin yankin, inda yake raba ribar kudinsu a wurin. A wurin, akwai masu kulawa da gonaki kamar Liu Sisheng guda 39, wadanda suke kula da rumfunan gonaki 105.
A shekarun baya baya nan, bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin gabashi da yammacin yankin, tunani, da ilmi daga gabashin yankin sun shiga yammacin yankin, kamar sabbin sha’ani, da hidimar al’umma da sauransu, wanda hakan ya taimakawa kauyuka masu talauci wajen samun farfadowa da saurin ci gaba. Ya zuwa karshen shekarar 2023, yankin Hongsibu dake kunshe da kauyen Hongde, ya taimakawa gidajen manoma fiye da 5300 wajen samun karin kudin shiga a fannin aikin noma, tare da kawowa mutane dubu 21 ayyukan yi.
Kafin a aiwatar da aikin yaki da talauci, akwai kauyuka masu talauci 40 a yankin Hongsibu, kuma yawan matalauta ya kai kashi 33 cikin dari, kana yawan matalauta a kauyen Hongde ya kai kashi 88 cikin dari bisa adadin mutanen kauyen, kana yawan kudin shiga na kowane mazaunin kauyen bai wuce kudin Sin Yuan 1800 kacal ba.
A halin yanzu kuwa, an samu nasarori a fannin raya aikin noma na musamman, kuma yawan kudin shiga da masana’antu ke samu yana karuwa da kashi 19.8 cikin dari a kowace shekara, har ma an gina sabbin gidaje da hanyoyin mota a yankin, yayin da kuma mazauna yankin suka samu yanayi na zaman rayuwa mai dadi.
A shekarar 1972, shirin samar da abinci na MDD wato WFP, ya taba ziyartar yankin Xihaigu, inda WFP ya ce wannan wuri bai dace da zaman rayuwar dan Adam ba. Amma a halin yanzu, wasu kauyuka masu samun arziki sun taimakawa sauran kauyuka wajen samun wadata tare a wannan yanki.
Cun Chao na lardin Guizhou ya shahara a duk fadin kasar Sin
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kan ce, a yi kokarin raya sha’anin musamman a kauyuka bisa yanayin da suke ciki, da sa kaimi ga raya sha’anin noma, da masana’antu da al’ummar kasar tare, don fadada hanyoyin samun kudin shiga na manoma.
A cikin wani yankin duwatsu dake lardin Guizhou, an shirya wata gasa ta kwallon kafa wadda ake yiwa lakabi da “Cun Chao” tsakanin manoma wadanda suke da zama a kauyuka ba tare da la’akari da kwarewa ba. Gasar Cun Chao ta sa kaimi ga wasan kwallon kafa ta yadda zai sake samun karbuwa a kasar Sin, kana ya wanzar da shahararsa a dogon lokaci ba kamar sauran wasanni ba. A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin neman kyautata tsarin raya Cun Chao, don kiyaye gudanar da gasar cikin nasara mai dorewa.
Gundumar Rongjiang ta taba zama gunduma mai fama da talauci a lardin Guizhou, kuma a baya ba a san gundumar sosai ba. Yawan mutanen gundumar bai wuce dubu 385 ba, kuma kashi 84.2 cikin dari ’yan kananan kabilu ne. Ko da yake yawan GDP na kowane mutum a gundumar a shekarar 2022 ya kai dubu 31, amma wannan adadi bai wuce kashi 1 cikin kaso 3 na yawan sauran wuraren kasar Sin ba. Lamarin da ya shaida cewa, tattalin arzikin gundumar bai samu ci gaba sosai ba idan an kwatanta da sauran sassan duk kasar Sin.
Domin daidaita wannan matsala, gwamnatin gundumar Rongjiang ta yi kokari a fannoni da dama, da yi namijin kokarin amfani da wasanni iri iri don farfado da tattalin arzikin gundumar, amma hakan bai samu nasara ba. Kana wadannan wasanni da gundumar ta shirya ba sa kunshe da wani abun ban mamaki na musamman, don haka ba su samu karbuwa sosai, da kuma jawo hankulan jama’a sosai ba.
Game da karbuwar Cun Chao, yawan masu bude ido a gundumar don kallon Cun Chao a shekarar 2023 ya kai miliyan 7 da dubu 660, kana yawansu ya kai ninka 20 bisa na mazauna gundumar, kana yawan kudin shiga da aka samu a sakamakon gasar Cun Chao a wannan shekara, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 8.4, yayin da yawan GDP na gundumar a shekarar ya kai kusan kudin Sin Yuan biliyan 9.6 kawai. Hakazalika kuma, gasar Cun Chao ta jawo masu kallo ta kafar intanet har biliyan 58, inda yawan masu kallon gasar a duk rana ya taba kaiwa mutane miliyan 100. A sakamakon hakan, kungiyar wasan kwallon kafa ta mashahuran mutanen yankin Hong Kong, da kungiyar wasan kwallon kafa ta ma’aikatan yankin Macao, da kungiyar wasan ta makarantar Yilan ta yankin Taiwan, da kungiyar wasan ta wakilan matasa ta kasar Faransa da sauransu, suka tafi gundumar Rongjiang domin halartar gasar ta Cun Chao.
Har zuwa yanzu, gasar Cun Chao ta riga ta shahara a ketare. Hukumar Premier League ta kasar Ingila, ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa tare da hukumar kula da gasar Cun Chao, don tattaunawa game da gudanar da gasar sada zumunta tare. Kana kasar Benin dake nahiyar Afirka ta koyi fasahohin shirya gasar Cun Chao, ta kuma kafa kungiyoyin wasan kwallon kafa na kauyuka 12, da gudanar da gasar Cun Chao ta nahiyar Afirka a ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2024.
Wannan ya shaida cewa, gasar Cun Chao ta samu karbuwa bisa kokarin jama’ar gundumar Rongjiang, da tunanin yin kirkire-kirkire. Ta hanyar wasan kwallon kafa, gundumar Rongjiang ta bude wata kofa ga duniya cikin nasara, kuma dukkanin sassan duniya na son sanin yadda gundumar Rongjiang take a halin yanzu.
Yawan mutanen kasar Sin ya zarce biliyan 1 da miliyan 400, abu ne mai wuya wannan kasa mai tarin mutane ta cimma burin samun wadata tare, wato dai akwai dawainiyar doguwar hanya da za a taka a wannan fanni, don haka aikin dake gaban komai shi ne yin la’akari da yanayin da ake ciki da bin hanya mafi dacewa.
Wadannan kauyuka uku sun taka hanyar samun bunkasa bisa hakikanin yanayin da suke ciki, ko da yake wasu sun samu wadata cikin sauri, wasu kuma sannu a hankali, amma dukkansu sun yi la’akari da yanayin da suke ciki, da neman amfani da fifikonsu da sabuwar hanyar samun ci gaba.
Ana bukatar jama’ar kasar Sin su dage da yin kokari don cimma burin samun wadata tare. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya yi bayani a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekarar 2025, cewar “Komai wahala burinmu zai cika idan mun yi kokari ba tare da kasala ba. Idan aka yi kokari sosai, za a cimma burin samun wadata tare a kasarmu”. (Zainab Zhang)