Karin kauyukan kasar Sin masu bude kofa ga ’yan yawon bude ido na samun karbuwa, da jawo ra’ayin al’ummun kasashen duniya daban daban. A kwanan nan ma karin irin wadannan kauyuka 4, sun shiga jerin “Kauyuka Mafiya Kayatarwa” na duniya na shekarar 2023, bisa jadawalin hukumar lura da yawon bude ido ta MDD ko UNWTO.
Sabbin kauyukan da suka shiga jadawalin a wannan karo sun hada da Huangling na lardin Jiangxi, da Xiajiang na lardin Zhejiang, da Zhagana na lardin Gansu. Sai kuma Zhujiawan na lardin Shaanxi. Kafin su akwai kauyukan Yucun na lardin Zhejiang, da Xidi na lardin Anhui, wadanda tun a shekarar 2021 suka yi nasarar shiga jadawalin na hukumar UNWTO.
Har ila yau, akwai kauyen Dazhai na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta, da Jingzhu dake karkashin birnin Chongqing, wadanda suka shiga jadawalin a shekarar 2022. Bisa hakan, kasar Sin mai irin wadannan kauyuka har guda 8, ta zamo ta daya a duniya a yawan “Kauyuka mafiya kayatarwa” na yawon shakatawa dake cikin jadawalin hukumar ta UNWTO.
Hakika yawon shakatawa muhimmin fanni ne na raya al’adu, da musayar su, da sada zumunta tsakanin al’ummun sassan duniya daban daban, kana wata dama ce ta nishadantarwa, da samar da kudaden shiga, da guraben ayyukan yi, wanda hakan ke raya tattalin arzikin duniya baki daya.
A fannin yawon shakatawa mai alaka da kauyuka kuwa, ma iya cewa hakan wata dama ce ta bunkasa ci gaban yankunan karkara dake sassa daban daban na duniya, kana hakan na baiwa al’ummun duniya damar kiyaye al’adun gargajiya da ake gada daga kaka da kakanni, ciki har da na kayayyaki, da wadanda ba na kayayyaki ba, da fannin noma, da kare kyakkyawan yanayin muhallin halittu da dai sauransu.
Ko shakka babu kasar Sin ta yi rawar gani a fannin inganta wannan sashe, musamman a shekarun baya bayan nan, inda har ma ma’aikatar raya al’adun kasa da yawon bude ido ta kasar, ta ce an kai ga kyautata kauyukan yawon bude ido a matakin kasa har guda 1,597, wanda hakan ya ingiza harkar bude ido a sassa daban daban na karkarar kasar.
Yayin da duniya ke mayar da hankali ga raya karin sassan tattalin arziki, da kyautata muhalli da muhallin halittu, fadada fannin yawon bude ido na kauyuka da Sin ke yi abun a yaba ne, kuma abun koyi ga kasashe masu tasowa da dama dake da irin wannan fifiko.